Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan sanda sun kama masu sanen waya a masallatan juma’a.

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane tara da ke satar wayoyin jama’a a masallatan juma’a musamman ma lokacin da ake tsaka da daura aure.

Kano Focus ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na runduna ‘yan sandan Abullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Lahadi.

Abdullahi Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce shugaban sashin Anti-daba Bashir Musa Gwadabe ne ya jagoranci sumamen da aka kama matasan.

Ya ce matasan na da kungiya da suke fita aiki duk ranekun mako, su kuma raba kansu masallatai da ke jihar nan domin satar waya lokacin da ake daurin aure.

A cewarsu basa yin amfani da makami, illa iyaka sun kwarene a bagaren sane kawai.

Ya ce sun kama mutum na farko ne a masallacin juma’a da ke Kofar Gadon Kaya, kuma shi ne ya bankado sauran wadanda aka tura sauran masallatan.

Yansanda a Kano sun kama wanda ya sassari matarsa a kotu

‘Yan sanda sun kama mace mai garkuwa da mutane a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta kama matasan da ke balle shaguna a unguwannin Kano

Idris Garba dan shekara 23 na daya daga cikin wadanda aka kama ya ce suna zuwa wuraren da ake daura aure ne a masallatai su yi sane.

Haka zalika Shima Yusuf Gambo mai shekara 25 wanda shi ne mai baburin adai-daita sahun ya ce shi yana jira ne da sun dauko sai su kawo masa ya tara.

Ya ce bayan sun sayar da wayoyin da aka samu ne kuma sai su raba kudin kowa ya samu.

Ya ce sun saci wayoyi ba adadi, ko kuma a takaice dai guda hamsi daga fara sana’arsu.

Shi ma wanda ake siyarwa da wayoyin Yusuf Balarabe dan shekara 24 ya ce idan sun sato suna kawo masa yana siya.

Ya ce ana kawo masa da daya da biyu yana siya, ya kuma kwashe wata bakwai yana sama’ar tare da su.

Yusuf ya ce tsahon wanna lokaci ya sayi wayoyi da dama a hannun su.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending