Connect with us

KANUN LABARAI

Rundunar ‘yan sanda ta kama matasan da ke balle shaguna a unguwannin Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin barayi ne dake balle shagunan al’umma tare da kwato wasu kayayyakin.

Kano Focus ta ruwaito wadanda ake zargin sun balle wani shago a unguwar Gwale tare da sace kekunan dinki guda biyar.

Haka kuma bayan bincike sun bayyana wadanda suke kaiwa kayan idan sun sata.

Wannan na kunshene cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Cikin wadanda ta kama akwai Naziru Haruna da ake kira Kwado mai shekaru 16 da Yusif Muhammad dan shekara 18, da kuma Abdulrahman Saminu shima mai shekaru 18 sai Halifa Iliyasu dan shekaru 14.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce haka zalika rundunar ta kama wasu dake siyan kayan da aka sato duk da cewa sun san kayan sata ne.

Ya kara da cewa wadanda aka kama da laifin siyan kayan  satar akwai Ibrahim Muhammad dan shekara 25 dake unguwar Sani Mainagge, da Isma’il Mohammed shima mai shekaru 25 mazaunin unguwar Sani Mainagge, sai Saminu Salisu dan shekara 34 dan unguwar Makwarari.

Ya kuma ce duk kan wadanda aka akama an same su dumu dumu da kekunan dinki na sata da suka siya.

Haka zalika ya ce rundunar ta kama wani mai suna Halifa Iliyasu dan unguwar Gwale mai shekaru 14 da ya balle shagon dinki a unguwar Sani Mainagge inda ya sace keken dinki da kayan sawa.

Ya ce rundunar ta kara samun nasarar kama wasu masu siyan kayan sata mazauna unguwar Sani Mainagge da suka hada da Saifullahi Ali mai shekara 24 sai Abduljabar Muhammed dan shekara 26.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda ya bayarda umarnin gudar da bincike tare da  gargadin al’umma da su guji siyan duk wani abu da ake zargin na sata ne.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending