Connect with us

KANUN LABARAI

Jin waka na kara imani- Ibrahim Khalil

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Kano dake Arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa jin waƙa yana ƙara nutsuwa, imani, ƙwazo da kuma zaburar da mutane.

Malam Khalil ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a wajen maulidin Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) na gidan Sheikh Malam Nasidi Abubakar Goron Dutse dake unguwar Goron Dutse a cikin birnin Kano.

Malamin, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ya ce: “Shi yasa da idan ana aikin gayya a kan kirawo Shafi’u, wani babban mawaƙi na Kano, da shi da masu kaɗa masa ganga, ana kaɗawa ana gangi ana waƙa, a kawo kunu a sha. Wasu lokuta ma a afa wani abu– ka ji garau, to a lokacin kai bai waye ba a lokacin, sai a dama a cikin kunu su sha, ka gan shi yana ta tsalle, har da to haka ake yi.

“To wannan saboda ɗan Adam, shi yasa za ku ga a cikin Sahihul Bukhari, lokacin da aka zo ana yin Masallacin Annabi (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi), da lokacin da ake haƙa Ramin Gwalalo, to ana rera waƙa, to Annabi ba ya rera waƙa, amma su sahabbai suna rerawa”.

Ya ƙara da cewa ana so kodayaushe a samu gwanin waƙa ya dinga rerawa saboda tana ƙara nishaɗi, tana kuma sabunta tunani.

“Don haka kada ka yadda ka haramta kanka jin waƙa. Idan ka ji wani mutum ya ce jin waƙa haram ne, haram ɗin da yake nufi waƙa da ake zage-zage, ake batsa, ake cin mutunci, ita ce haram, ita ce take kashe zuciya.

“Amma wadda za a yabi Annabi, ko a yabi abubuwa masu kyau ko zance mai daɗi; ita waƙa kamar magana ce, mai daɗi mai daɗi ce, mara daɗi mara daɗi ce, kalmomi masu kyau masu kyau ne, marasa kyau marasa kyau ne.

“Don haka waƙa ba mummunar aba ba ce, sai dai idan akwai zage-zage, ko sharri ko cin mutuncin mutane, ko batsa, to wannan ita ce ba a so. Amma kada ku haramta kanku jin waƙa, musamman Ishiriniya, da raguwar waƙoƙi da ake yi cike da hikima da basira”.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending