Connect with us

KANUN LABARAI

Martani ga al’ummar Yarabawa, da batun karfafa hadin kan kasa

Published

on

Alhaji Tanko Yakasai
Share

Alhaji Tanko Yakasai

A watan Disamba na shekarar 2016, an shirya wata mukala domin a tayani murnar cikata shekara 90 a duniya. A wannan lokaci ya zama kamar al’ada idan za a yi bikin ranar haihuwata a gabatar da makala domin tayani murna.

Amma tun daga shekarar 2016 da ya zama kowa ma na irin wannan taron domin murnar ranar haihuwarsa sai muka daina.

Sai dai lokacin da aka zo bikin cikata shekara 90 a duniya wani takwarana Salihu, wanda na ambaceshi a cikin rubutun tarihina, ya gano wasu kusakurai dangane da shekarar da aka haifemu.

Salihu ya girmeni da kwanaki 40, ya ce an haifemu a lokacin mulkin Sarkin Kano Usman dan Majekarofi a shekarar 1925, ba lokacin Sarkin Kano Abdullahi Bayero ba.

Ya ce ba wai kawai iyayensa sun gaya masa hakan ba, hatta bayanan da aka dauka lokacin da suka shiga elemantare ta Shahuci ya nuna hakan.

Wannan abu da dan uwana ya bankado ya karfafamin gwiwa wajen shiga bincike domin gano inda aka samo matsalar shekarar da aka haifeni.

Na fara bincikenne daga shekarar da na yi aure. Kamar yadda na rubuta a cikin tarihina, na yin auren fari ne a shekarar 1945 wanda a shekararne aka kawo karshen yakin duniyan na II.

Na tabbatar na yi auren fari ina dan shekara 20 dai-dai, bugu da kari na tabbatar munyi aure rana daya da Alhaji Sabo Dan Galadiman Tangar.

Allah kuma ya albarkanceshi da samun dansa na fari a shekarar 1946, a don haka shima bayanan rayuwarsa zai taimaka wajen gane hakikanin sanda aka haifeni.

Wadannan dalilai sun tabbatarmin cewa shekarar da aka haifeni ita ce 1925 ba 1926 ba, da kuma wannan ne na sauya shekarar haihuwata zuwa 1925.

Ina godewa Allah da ya bani dama na sake gani zagayowar ranar haihuwata.

A baya manyan mutane ake gayyata domin su yi jawabai a bikin ranar haihuwata, amma a bana ba za a iya hada wannan taro ba biyo bayan barkewar cutar Covid-19 a duniya baki daya, da kuma tsarin tazara da aka bullo dashi.

Bisa wannan dalili ne a wannan shekara na zabi na yi bayanin kan al’amuran da ake ciki a kasa baki daya. Haka kuma na zabi abinda nake ganin ya fi zama muhimmanci a yi magana a kai da ya dade yana cin tuwo a kwarya.

Wadannan abubuwa sun dade suna jawo tafka muhawara acikin jama’a.

Abubuwan kuwa sun hadar da batun yin gyara a kundin tsarin mulki da kuma kuma batun kidayar al’umma ta kasa.

Gyaran kundin tsarin mulkin kasa

Idan za a iya tunawa a ranar 11 ga Satumba, 2020 kungiyar al’ummar Yarabawa ta yi taro a Legas ta kuma tattauna batutuwa masu muhimmanci da suka shafi kasa, a kokarinsu na samar da kasa da za ta maida al’amranta kan Yarabawa.

A karshen taron, sun fitar da bayanin bayan taro, da suka bayyana matsayarsu kan batun da suka shafi kasa, da suka hadar da sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasa, kidayar al’umma da kuma batun samar da hanyoyin ruwa da wasu batutuwa masu muhimmanci.

To akan wannan ne na ke son yin amfani da damar wajen fito da muhimman batutuwa da za su yi karin haske kan bukatun da suka bijiro da su a jawabin su na bayan taro.

Zan kuma fara da batun sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasa wanda yanzu haka ana tattauna batun a zauren majalisar kasar nan.

Kungiyar ta Yarabawa ta bukaci da a yi watsi da kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 wanda suka kirashi da ‘kundin tsarin da ba a shirya shi domi magance matsalar kasa ba’ bisa fakewa da cewa ya samo asaline daga tsarin mulkin soji, da suke gani na danne wasu daga cikin manufofin al’ummar kasar nan musamman ma na kudanci.

Galibin wadanda suka yi gyara kundin yan kudu ne

A kokarina na amsa wannan, bari na danyi ratse zuwa wani tarihi musamman na yadda Abdussalam Abubakar ya kawo kundin tsarin mulkin kasa na 1999.

Za mu iya tunawa, bayan da Abdussalam Abubakar ya zama shugaban kasa, ya kafa wani kwamiti da zai yi nazarin kundin mulkin kasa da Justice Niki Tobi ya jagoranta, wanda daga kudancin kasar nan ya fito.

Bayan da kwamitin ya kewaya lungu da sako na kasar nan domin jin ra’ayoyin jama’a, ya mika rahotonsa inda ya ce galibin al’ummar kasar nan basa goyon bayan sake sabun kudin tsarin mulkin kasa.

 

Hakan ya sanya kwamitin ya bada shawarar a yiwa kundin tsarin mulkin kasa na 1979 kwaskwarima a wadannan bangarori.

  1. a kara adadin jihohin kasar nan daga 19 zuwa 36 a shekarar 1999.
  2. Samar da hukumar tabbatar da dai-daito a tsakanin al’ummar kasar nan a ayyukan gwamnati
  3. da kuma batun karuwar al’umma da saura batutuwa.

Sai dai bayan da kwamitin ya kammala aikinsa, ba wani abu mai yawa aka kara ko aka shigar a cikin kudin tsarin mulkin ba.

Tun bayan da aka fito da sabon kundin tsarin mulkin da aka yiwa gyara, gidan jaridar Thisday suka kafa kwamitin editoci uku domin su nazarci kudin biyu domin ganin ko da akwai banban ci ko babu.

A karshen aikin nasu daya daga cikin wadanda suka yi akin Simon Kolawole ya wallafa wani rubutu da ya yiwa take da “wannan abun da ake kira kundin tsarin mulkin kasa na 1999”.

Ya ce kwamitinsa ya yi karatun ta nutsu kan kudin tsarin mulkin biyu daga bango zuwa bango, inda kuma suka ce banda wadansu abubuwa kalilan da aka dan sauya amma ba a sauya komai daga kundin na shekarar 1979 ba.

Abin lura a nan shi ne kundin tsarin mulki na 1999 da ake mafani da shi dan gyara ne kawai daga kundin tsarin mulkin kasa na 1979.

Haka kuma fitattun mutane ne da suka fito daga dukkani bagarotin kasar nan suka amince da sabon kundin tsarin mulkin, da suka hadar da

a – Dr Nnamdi Azikwe na jam’iyyar NCNC a jamhuriyya ta farko kuma shugaban NPP a shekarar 1979.

b-Chief Obafemi Awolowo na jam’iyyar Action Group (AG) a jamuriyya ta farko kuma  ds kums UPN a jamhuiryya ta biyu;

c- Malam Aminu Kano na jam’iyyar (NEPU) a jamhuriyya ta farko kuma mamba a jam’iyyar PRP a shekarar 1979

d- Comrade Waziri Ibrahim na NPCd da kuma (GNPP) a shekarar 1979.

e- Chief Joseph Tarka na UMBC  ita ma a jamhuriyya ta farko da kuma NPN a shekarar 1979.

f- Chief Harold Dappa Bitiye da Chief Milford Okilo da suka fito daga jam’iyyar (NDC) a jamhuriyya ta farko kuma suka zama mambobi a NPC a jamhuriyya ta biyu.

Yana da kyau mu fahinci cewa wadannan shugabannin da suka fito daga dukkanin bagarorin kasar nan sun amince da kundin tsarin mulkin da aka samar, kuma galibinsu sun tsaya zaben a karkashin kudin tsarin mulkin shekarar 1979 da sojojin suka samar.

A cikin shugabaninmu na farko da suka jagoraci kasar nan Sir Abubakar Tafawa Balewa da kuma Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ne kawai basa raye lokacin jamhuriyya ta biyu.

A don haka ba dai-dai bane kungiyar Yarabawa ta kalubalanci kundin tsarin mulkin kasa har ma su kirashi da ‘kundin tsarin da ba a shirya shi domi magance matsalar kasa ba’ inda suka fake da cewa sojoji ne suka samar da shi.

Kidayar al’umma

Abu na biyu kuma da ke da matukar muhimmanci shi ne batun kidayar al’umma, kwamitin Yarabawa da sauran al’umma da suka fito daga kudancin kasar nan sun soki adadin al’ummar da akace kasar nan na da shi.

A cewarsu Burtaniya ta fifita arewacin kasarnan lokacin da aka gudanar da kidaya.

Akan wannan batun ma baru mu koma baya mu nazarci abinda ya faru.

Mu fara da batun kidaya ta farko da akayi a kasarnan a shekarar 1911 wadda ita ce ta kawo hadewar bagaren kudanci da kuma arewaci a shekarar 1914.

Kidayar da aka fara yi ta farko a kasar nan anyi ta ne a shekarar 1911, kuma lokacin da aka gudanar da ita Burtaniya ba ta da ikon gudanar da kidayar a bagarorin biyu da suka samar da kasar nan saboda rashi kudi, da kuma kayan aiki

A don hakanne suka yi amfani da adadin wadanda ke biyan haraji a wancan lokaci suka kuma fitar da adadin al’ummar yankunan biyu. Haka zalika irin hanyar dai akabi wajen gudanar da kidayar jama’a a shekarar 1921 da kuma 1931.

Amma ba a gudanar da kidayarba a shekarar 1941 sakamakon barkewar yakin duniya na II har sai a shekarar 1952 da kuma 1953.

Dukkanin wadannan kidaya an gudanar da su ne kafin samun yancin kai, da kuma kidayar ta nuna arewacin kasar nan na da kaso 54 cikin dari inda kudancin kasar nan ke da kaso 46 cikin dari na adadin al’ummar kasar nan.

Ga misali adadin al’ummar kasar nan da ake da su  a shekarar 1911 shi ne milyan 18 da dubu 72, inda kuma arewacin kasar nan ke da milyan miliyan 10, yayinda kudancin kasar nan ke da milyan 8 da dubu 16.

Bugu da kari a shekarar 1921 kidayar da aka yi ta nuna cewa arewacin kasar nan na da adadin mutane milyan 10 da dubu 26 da hakan ke nuna suna da kaso 55 cikin dari, yayin da kdancin kasar nan ke da mutane milyan 8 da dubu 63 da hakan ya kunshi kaso 44 da digo tara.

Haka kuma a shekarar 1931 adadin al’ummar kasar nan shi ne miliyan 19 da dubu dari 9, inda arewacin kasar nan ke da milyan 11 da dubu 43, yayin da kudanci ke da milyan 8 da dubu 4.

Haka zalika a shekarar 1952 da 1953 lokacin da aka gudanar da kidaya ta farko da aka kirga mutane, adadin al’ummar ya nuna kasar nan na da mutane milyan 31 da dubu dari, inda arewacin kasar nan ke da milyan 16 da milyan takwas yayin da kudancin kasar nan ke da milyan 14 da dubu dari uku.

Kidaya domin karbar haraji

Yana da matukar muhimmanci mufahinci cewar kidayar al’umma da aka yi kafin ‘yancin kai anyitane kawai domin karbar haraji, amma batun rabon arikin kasa da wakilci akan adadi yazo bayan da aka samu yancin kai.

A don haka arewacin kasar nan ba shi da wani iko ko kuma yunkuri kara adadin al’ummar da yake da shi, haka zalika turawan mulkin mallaka basu da wani dalili da zaisa su fifita arewacin kasar nan a kan kudanci saboda a shekarar 1911 babu wani abu da ake kira Najeriya.

Bayan samun ‘yancin kai, an gudanar da kidaya a kasar nan a shekarun1963 da 1973, da kuma 1991 sai kuma shekarar 2006.

Sai dai gwamnatin yammacin kasarnan a wancan lokaci ta kalubalanci kidayar, amma dai daga baya aka sasanta aka kuma sake wata kidayar a shekarar 1963 da kowa ya aminta da ita.

Jadawil : yadda aka gudanar da kidaya daga shekarar1911-2006

Shekara       Arewa            Kudu

1911           55.00%        45.00%

1921           55.10%        44.90%

  1.           57.40 %       42.60%

1952           54.55%        45.45%

1962           56.77%        43.23%

1963           53.51%        46.49%

1973           64.99%        35.01%

1991           51.85%        48.15%

2006           53.59%        46.41%

Ba a kidaya mata a Arewa

Abinda ya fi muhimmanci a fito da shi a nan shi ne kafin samun ‘yancin kai mata a arewacin kasar nan basa cikin wadanda ake kidayawa.

Hakan ya farune sakamakon duk wanda aka kidaya a na sa ran zai biy haraji, kuma matan arewa basa biyan haraji, sabanin matan kudu.

Harajin da matan kudancin nan ke biya shi ne ya jawo zanga-zangar mata a Onitsha a shekarar 1953, inda suke ganin kamar an kara adadin yawansu da gangan domin a tara haraji.

Wannan ya nuna cewa adadin al’ummar arewacin kasar nan da ya ke tsayawa a kaso 50 kafin yancin kai ya fi haka, sai dai ya karu bayan da aka samu ‘yancin kai da aka fara kidayawa da matan arewacin kasar nan.

Daga shekarar 1951 zuwa 1959 aka shigo da tsarin wakilci a cikin gwamnatin kasar nan, haka kuma aka fara bada mukamin minister akan tsarin wakilci.

A wannan lokaci kafatanin arewacin kasar nan suna da ministoci hudu ne kawai, inda kuma kudancin kasar nan ke da 9, hudu da ga yamma, hudu daga gabas, sannan daya daga kudanci kamaru.

Za a iya cewa rashin sanya matan arewacin kasar nan a cikin kidaya ne ya kawo karancin samun ministoci daga arewacin kasar nan lokacin turawan mulkin mallaka.

La’akari da abinda aka ambata, wannan ya tabbatar da cewa duk wani ikirari da wata kungiya za ta yi ko wani mutum na cewa turawan burtaniya sun fifita arewacin kasarnan wajen kidaya ba gaskiyabane tarihi ma ya tabbatar da haka.

Ba a kan kidaya kawai aka kirkiri kananan hukumomi ba

Abu na uku da kungiyar ta Yoruba suka ambata shi ne jihar Legas da Kano kusan daya suke a fagen al’umma, amma jihar Lagos na da kananan hukumomi 20 Kano nada 44, hakan ta sanya suka ce an fifita Kano ya yin kirkirar kananan hukumomi.

Da wannan ne kuma na ke so ku fahinci cewa kirkirar kananan hukumomi ba a yi shi kan tsarin adadin al’umma kawai ba har ma da girman kasa.

Hakan ce ta sanya jihar Kano da ke da girman kasa da ta kai fadin murabba’i dubu 20, 131 ta ke da kananan hukumomi da suka fi na Lagos da ta ke da fadin murabbu’i 3, 345.

Wannan dalili da aka ambata da yake ta jawo cece-kuce ake kuma ta jifan juna da maganganu na da cikin abinda nima ke cimin tuwo a kwarya.

Abinda na fahinta shi ne irin wadannan kalamai ba abinda suke haifarwa sai kara raba kan kasa.

Rikicin samun yancin kai

Wadannan kalamai sun yi dai-dai da wata bukata da ta jawo cecekuje a malisar kasa a shekarar 1956.

Inda wani wakili daga jam’iyyar Action group ya gabatar da kudirin neman samun ‘yancin kai daga hannun turawan burtaniya a shekara a shekarar 1956.

Haka zalika wani wakili daga arewacin kasar nan shima ya gabatar da nasa kudirin da ke kalubalantar na baya, cewar bai kamata a bada ‘yancin kai a shekarar 1956.

Wannan kuwa ya faru ne kasancewar a duk fadin arewacin kasar nan mutun daya ne ke da degree wato Dr R.A.B Dikko.

A wannan lokaci kudancin kasarnan na da masu digiri sama da dubu a bangarori daban-daban da suka hadar bangaren Injiniya, likitanci sha’anin mulki da kuma zamantakewar al’umma da na Lauya.

Haka kuma kusan kaso casa’in na masu aiki a arewacin kasar nan sun fito ne daga kudanci.

Haka zalika wakilai daga Action Group suma sun soki bukatar kin bada ‘yancin kai a shekarar 1956 a cewarsu hakan baiwa yankin arewa damane su kara shiri.

Dalilin hakan, shi ne idan Najeriya ta samu ‘yancin kai a shekarar 1956 zai kasance dgalibin wadanda za su yi aikin gwamnati a arewacin kasar nan za su fito ne daga kudanci, yanayin da ake ganin zai jefa arewacin kasar nan karkashin ikon kudanci, musamman ma mutanen da suka fito daga yammacin kasarnan da su ke da adadin mutane da suka fi yawa a cikin gwamnati.

Wannan yanayi da aka tsinci kai ya yamutsa hazo kuma ya ci gaba da zama tushen tashin hakali na har abada da ba zai taimka wajen ci gaban kasa ba.

Kuma wannan da alama shi ne tushen gabar da ta kullu tsakanin magoya bayan jam’iyya Action grourp akan al’ummar arewacin kasar nan da har zuwa wannan lokaci take ruruwa.

 Al’ummar kudu sunfi amfanuwa da Najeriya

A baya-bayan nan na karanta wani rubutu da aka wallafa a Internet da ke nuna cewa kaso 80 cikin dari na masu arzikin kasar nan sun fito ne daga kudanci.

Haka zalika yananan a rubuce cewa yanayin talauci da yunwa a kudancin kasar nan ko kadan bai kai na arewaciba, da ya nuna cewa arewa na da kaso 65 cikin dari na talakawan kasar nan.

Wannan ya nuna karara cewa abokan zamanmu da ke kudancin kasar nan sun fi amfanuwa da kasar nan fiyeda mu da muka fito daga arewacin kasar nan, duk da haka al’ummar arewacin kasar nan basa korafi kan wanna wawakeken gibi, duk da cewa dayawa daga cikin arzikin kasa suna kudancin kasar nan.

Watakila abinda ya sa al’ummar Arewacin kasar nan basu damu da abubuwan dake kuduba, sun fahinci cewa arzikin al’umma ya fi kowanne irin arziki.

Zan iya tunawa shekara 60 da suka wuce lokacin da naje kasar China, yanayin ci gaban kasar kusan irin daya ne da na Najeriya a halin yanzu.

Sai dai yau kasar China, ita ce kasa ta biyu bayan kasar Amurka a duniya ta bangaren tattalin arziki da sauran bangarori na rayuwa.

A don haka babu wani dalili da za a ce kasar nan na da ma’adanai da tattlain arziki da ba za su habaka ci gaban kasar nan ba, da kuma kowa zai amfana da shi.

Rashin bada dama wajen habaka al’amura da kuma dakile batun ci gaba kullum ke rura wutar halin da ake ciki a yanzu.

Abinda muke bukata shi ne shugabanin da za su sadukar da kansu, kuma wadanda za su iya, domin su ciyar da kasar nan gaba.

Akwai bukatar kafa jam’iyyun siyasa na gaske

Da wannan ne kuma nake cewa, sai ansamu jam’iyyar siyasa mai karfin gaske da take da hangen nesa wajen gina kasa, za a iya samar da shugabannin da ake bukata.

A don haka muna bukatar jam’iyyun siya da al’umma suka yarda da su wadanda suka shirya domin tunkarar abinda al’umma suke bukata.

Jam’iyyar Action Group ita ce wadda ya kamata a ce ta samar da wannan bukata , ta yi kokarin fahitar da al’ummar kasar nan cewa an kafatane domin al’umma da suka fito daga dukkanin bagarorin kasar nan.

Sai dai abin takaicin shi ne dukkanin shugabanninta da ma jam’iyyar da ta gajeta ta UPN sun mai da hankali ne kawai wajen ciyar da al’ummar Yarabawa gaba, mai makon kasa baki daya.

Manyan mutane da suka shiga jam’iyyar ta AG da UPN daga Arewacin kasar nan an basu manya mukamai, amma sai aka mayar da su saniyar ware, da hakan ya sanya suka zare jikinsu a hankali.

Wadannan manyan arewa masu son cigaba da suka shiga jam’iyyar sun hadar da Abba Maikwaru, Malam Ibrahim Imam, Hon Muhammad Basharu, Malam Jamo Funtua, J S Tarka, Chia Surma.

Sauran sun hadar daPartic Dokotri, Sen. Ibrahim Dimis, Jonah Assadugu, Malam Yabagi Bidda, Alh Maito na Ilorin, Sen Abaagu daga Benue, Malam Maiyaqi daga kudancin Zaria, Malam Haruna Wakilin Doka doga Sokoto, Mr Philip Maken daga Ganye, Peter Gawon, yayan shugaban kasa Gen. Yakubu Gowon da kuma Malama Ladi ‘Yartakarda.

A yanzu irin wadannan shugabanin na AG da UPN daga yankin Yarabawa sun zama yan burbushi a kasar nan, koma babusu.

Haka kuma akwai mutane da yawa da su fito daga wasu jam’iyyu a kudanci da yammacin kasar nan da suka maida hankali wajen cigaban al’umma, da suka hadar NCNC da NPN, da ya kamata a karfafa musu gwiwa.

Bayan godiya ga Allah kan kyautar rayuwa da ya bamu, ya zama wajibi akan shugabanni, da sauran masu fada aji su kaucewa duk wani abu da ka iya kawo rudani a cikin jama’a, su kuma samarda hanyoyin da za rayu cikin zaman lafiya da hadin kan kasa.

Arewa ta samar da kugiya mai karfin gaske

Al’ummar arewacin kasar nan ya kamata su taimaka wajen samarda wata kungiya mai karfi da zata taimaka wajen samun hadin kan kasar nan ta hayar hada kai da sauran bangarorin kasa.

Tabbas ya zama dole Arewacin kasarnan ya ci gaba da lalubar mutane masu hangen nesa, kuma suke da kwarewa, suke kuma da son yankin a zuwciyarsu, su samar da wata hanya da zai kawo sauki ya kuma rage radadin talaucin da ake ciki a arewacin kasar nan.

Idan aka yi haka lallai al’ummar kudancin kasar nan za su yaba da irin rawar da Arewa ta taka wajen ci gaban kasa, kawo kwaciyar hankali da ci gaba al’umma.

Nagode Allah ya yiwa kasa ta Najeriya albarka

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending