Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan wasan Hausa a Kano sun yi tofin alatsine ga shugaban Faransa

Published

on

Share

Aminu Abdulahi

Wasu daga cikin jaruman Kannywood a nan Kano sun  yi tofin alatsine ga shugaban kasar Faransa Emanuel Macron bisa nuna goyan bayansa kan batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Manzon Allah (S.A.W.)

Kano Focus ta ruwaito jaruman na ci gaba da yin tofin alatsine ne a shafukansu na Instagram, Twitter da kuma Facebok.

Emanuel Macron dai ya fito fili ya nuna goyon bayansa kan zanen barkwanci da wani kamfanin kasar Faransa ya wallafa  kuma siffantashi da Annabi (S.A.W), da wani malami a kasar ya yada shi ga dalibai.

Wannan dalili ne ya sanya musulmi a fadin duniya ke caccakar shugaban kasar ta Faransa bisa goyon bayan da ya bayar na cin zarafin annabin rahama.

Cikin dubban masu yin tofin alatsinen har da juramai da masu shirya fina-finan Hausa da suka dinga yin rubutun tsinuwa, wasu kuma suna wallafa hoton bidiyo da tsinuwa ga Emanuel Macron.

Falalu A Dorayi 

Falalu Dorayi mai bada umarni ne kuma mashiryin fina-finai, cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bukaci jama’ar muslmi da su tsinewa shugaban kasar ta Faransa da ‘yan koransa.

Ya kuma ce jihadi ne jama’a su yi iya kokarinsu na la’antar sa, musamman ma a shafukansu na sada zumunta.

A cewarsa abin kunyane a ce matasa sun kasa yin yin wani rubutu a shafukan su na sada zumunta da zai kare martabar shugban hallitta.

“Idan har zaka iya yin rubutu ko saka bidiyo don taya kanwar ka ta Likoro ko Fandogari murnar zagayowar ranar haihuwar ta, ko taya abokin ka murna idan wani abu ya same shi, amma ‘dan karamin rubutu da za kayi kace kana nuna bakin ciki kan masu cin zarafin manzon Allah S.W.A  sai ya gagara, wannan abin takaici ne” inji Falalu.

Ali Nuhu

Shi ma guda cikin jaruman fina-finan Hausa Ali Nuhu ya wallafa wani rubutu a shafin sa na Facebook da ya yi yabo ga fiyayyen halitta tare da yin tsinuwa ga masuyin batanci ga shugaban halitta Manzon Allah S.W.A.

“Ya Rasulallah S.A.W. Kai Rahmane garemu a duniya kai Rahma ne gare mu a Lahira.

“Muna sonka fiye da kanmu, da Iyayenmu, da ‘Ya’yanmu, muna sonka fiye da duk abinda muka mallaka.

“A shirye muke mu bayar da jininmu akan ka ya Rasulallah.

“Allah kai tsinuwa ga duk wanda sukai batanci ga Annabin mu Muhammad S.A.W Allah ka wulakantar da su tun anan duniya  #WeLoveMuhammad,” inji Ali Nuhu.

Haruna Salisu (Cizo)

Shima daya daga cikin mawaka a masana’antar mai suna Haruna Salisu da ake kira ‘Cizo One Germany’ ya yi kira ga al’ummar musulmi da su kauracewa siyan duk wani abu wanda ya kasance mallakin kasar Faransa ne.

Ya ce matukar al’ummar musulmi suka kauracewa siyan kayayyakin da ake sarrafawa daga kasar tabbas hakan zai sa kasar ta shiga taitayin ta.

Ya kara da cewa addinin musulunci addinine dake  son zaman lafiya hakan ta sanya mulunci ke mutunta kowane addini a duniya.

Umar Nagudu

Mawaki Umar Adam Gambo Nagudu ya wallafa bidiyo a shafin sa na Instagram inda ya yi kira ga sauran mawakan Hausa da al’umma da su sani cewa kare mutunci da martaba ta manzon Allah shi ne gaba da komai.

Nagudu ya ce da yawan mawaka sunki cewa komai kan batancin da akayiwa ma’aiki duk kuwa da irin lokutan da suke shafewa a kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa babu amfanin cigaba da kasancewa a kafar sada zumunta da wasu jarumai da mawaka keyi matukar ba za su fito su nuna fushinsu ga irin cinkashin da akeyiwa al’ummar musulmi ba.

“Wani zaka samu yana da mabiya a kafa guda daya da suka haura miliyan biyu.

Kullum yana kasancewa tare dasu, amma ba zai iya yin rubutu na minti biyu ba don yin Allah wadai da abubuwan dake faruwa.

“Wannan abin kunya ne kuma kalubalene a garemu.” a cewar sa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su hade kansu, a cewarsa ta hakane kawai za su iya kawo karshen cin kashin da kafirai kewa musulmi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending