KANUN LABARAI

Kofin kalubale: Jara’af ta lallasa Kano Pillars da ci 3 da 1

Published

on

Share

Ahmad Hamisu Gwale

Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars tayi rashin nasara a hannun takwararta ta ASC Jara’af da ci 3 da 1 a gasar kofin kalubale na nahiyar Africa wato (CAF Confederation) da aka fafata a jiya Asabar.

Kano Focus ta ruwaito ya yin wasan na jiya Pillars ce  ta fara zura kwallan farko a minti na 12 ta hannun dan wasanta   David Ebuka.

Kafin daga bisani dan wasa  Zakky Bassane ya ramawa Jara’af kwallan da aka zura musu a minti na 17.

Haka kuma  dan wasa  Samba Diallo ya kara wa Kano Pillars kwallo ta biyu a minti na 38.

Haka zalika dan wasa Libasse Gueye ya tabbatar da nasarar kungiyar bayan zura kwallo ta uku da ya yi aminti na 80, mintina goma kafin tashi daga wasan.

Sai dai bayan kammala wasanne na jiya kyaftin din kugiyar kwallon Kafa ta Kano Pillars Rabi’I Ali ya ke cewa har yanzu suna da karsashi kan was an.

A cewar sa suma idan an dawo nan gida Najeriya ba ko shakka za su rama kwallayen su harma su samu Nasara.

Ya kuma bukaci magoya bayan kungiyar ta Kano Pillars da kada gwiwarsu ta yi sanyi, a cewarsa baya dar din samu Nasara a wasansu na gaba.

Ana saran a mako mai zuwa kungiyar kwallan kafa ta Kano Pillars za ta karbi bakuncin Jara’ar a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna domin buga zagaye na biyu na gasar.

Click to comment

Trending

Copyright © 2020 - KANO FOCUS - NIGERIA