Connect with us

Uncategorized

Yadda karancin ruwa da kwari ke illata harkar Noma a Najeriya

Published

on

Share

Gwamnatin Kano ta ce noma na samun koma baya sakamakon karuwar kwari da ke lalata albarkar noma da kuma karancin ruwa da ake fama da shi sakamakon sauyin yanayi.

Kano Focus ta ruwaito mataimakin gwamnan Kano, kuma kwamishinan noma Nasiru Yusuf Gawuna ne ya bayyana hakan yayin taron karawa juna sani tsakanin ‘yan jarida da masana kimiyya noma da malaman gona a Kano.

Gawuna ya ce kananan manoma na fama da rashin ingantaccen kayan gona da rashin wadataccen irin  da hakan ke kawowa harkar Noma cikas a kasar nan.

Ya kara da cewa Najeriya za ta zarta sauran kasashe wajen samar da abinci matukar  an rungumi fasahar inganta noma a kimiyyance.

A cewarsa, yayin da sauran kasashe ke fitar da tan 10 na hectar masara, a Najeriya mafi yawan da ake fitarwa baya wuce tan 4.

Haka kuma  yayin da ake samar da rogo na kimanin tan 4 sauran kasashen na samar da kimanin tan 13, ya yin da wake shima ke samun wannan koma bayan.

Ya kara da cewa suna da yakinin shigowar kungiyar da ke wayar da kan manoman kan fasahar harkokin noma wato (OFAB) Najeriya za ta kawo karshen matsalar.

Da yake nasa jawabin shugaban hukumar bunkasa fasahar tsirrai da dabobbi ta kasa wato NABDA farfesa Abdullahi Mustapha ya jadadda alfanun kafafan yada labarai wajen taimakawa jama’a su fahinci fasahar da hukumar ke samarwa ga manoma.

Haka kuma ya ce manoma za su fuskanci yadda za su bunkasa harkar  samar da abinci da kaucewa matsalolin da su ke fama da shi.

Ya ce a shekarun baya mutane da dama basu aminta da fasahar da suke kirkirowaba na kimiyya sakamakon mafi yawan binciken masana kimiyya baya isa ga al’umma.

IAR ta samar da irin masara da ke jure fari, kuma tsutsa ba ta ci

Ya ce arewacin Najeriya na daya daga cikin yankunan da suka fi kowa harkokin noma, mussamam wajen shuka wake, auduga.

Kuma an samu wannan cigabanne da taimakon yan jaridu da har ta kai manoman sun aminta da sabbin binciken da ke fitowa.

Farfesa Abdullahi ya kara da cewa Najeriya ita ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta samar da ingantaceccen irin wake, wanda yake jure karancin ruwa sannan kwari basa iya yi masa illa.

Anata bangaren shugabar da ke kula da kungiyar da ke wayar da kan manoman kan fasahar harkokin noma OFAB Dr Rose Gidado ta ce suna gudanar da ire-iren wandanan tarukan ne don  wayar da kan manoma da masana alfanun fasahar zamani domin inganta noma.

Ta ce tuni aka baiwa manoma ingantancen irin wake da suka shuka suka kuma samu yabanya mai kyau.

Haka kuma manoma auduga za su samu na su irn na zamani karshen wannan watan.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya dakatar da Abduljabbar Kabara daga yin wa’azi

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara daga yin wa’azi, tare da bada umarnin rufe masallacinsa.

Kano Focus ta ruwaito kwamishinan yada labarai  na jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan a daren Laraba.

Kwamishinan ya ce an dauki matakin kulle masallacin  ne saboda dalilan tsaro.

cikkaken labarin na tafe……

 

Continue Reading

KANUN LABARAI

PDP a Kano ta ce ba za ta shiga zaben kananan hukumomi ba

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyar PDP, a Kano ta ce ba za ta shiga a fafata da ita ba a zaben kanan hukumomin jihar nan da ke tafe.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kwamitin riko na jam’iyyar, DanLadi Abdulhamid ne ya bayyana hakan ya yin taron manema labarai a ofishin jam’iyyar dake  nan Kano.

Danladi Abdulmumin ya yi zargin cewa an fitar da kudaden da suka wuce kima wajen yin zaben sannan kuma suna tsoron haifar da rikici yayin zaben.

Ya ce babu yadda za yi su shiga zaben da tuni Gwamnan Kano Ganduje ya rubuta wadanda za su ci.

Ya kuma ce gwamnati ta ware kudi kimanin naira biliyan biyu da miliyan dari uku kan zaben da sun riga sun san su za su baiwa kansu.

tuni dai hukumar zabe ta jihar Kano ta sanar da watan Janairun badi a matsayin watan da za ta gudanar da zaben kanan hukumomi da na kasila a fadin jihar nan

Continue Reading

GAME DA MU

Yan sanda a Kano sun sake kana dan sahun da ke sauke fasinja ya gudu da kayansu

Published

on

Share

Aminu Abdulahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake cafke direban adai-data sahu da ya kware wajen guduwa da kayayyakin fasinjoji ya yin da yake tuki.

Kano Focus ta ruwaito cewa an sake cafke direban adai-daita sahun ne mai shekaru 39 bayan da ya sake yin batan dabo da kayan wasu mata na kimanin naira dubu dari hudu a bakin barikin Bokabo.

Direban adai-daita sahun mai suna Muhammad Ahmad Muhammad Kabuga ya ce wannanne karo na biyu da aka sake kama shi da aikata irin wannan laifi.

Ya ce kaddarace ta sa shi yake aikata irin wannan muguwar dabi’a kuma yana fatan Allah ya shirye shi.

A nasa bangaren mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sati biyu da suka gabata suka kama wanda ake zargin tare da gurfanar dashi a gaban kotu.

Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce kotu ta yanke masa hukuncin shekara biyu ko kuma biyan tarar naira dubu arba’in wanda kuma ya biya tarar nan take.

Saidai bayan da ya fito ne kuma sai ya sake yin awon gaba da kayayyakin wasu mata su biyar.

Kiyawa ya kuma ce wanda ake zargin ya tabbatarwa da rundunar cewa ya aikata duk kan lefukan da ake tuhumar sa da shi.

Ya kara da cewa bayan da suka ci gaba da bincike ne kuma sai suka same shi da jabun kudi kimanin naira dubu hamsin.

Ya kuma tabbatar da cewa yana siyan rafa daya a gurin wasu mutane akan naira dubu goma sha biyar kana daga bisani kuma ya shiga dasu cikin kasuwa.

Continue Reading

Trending