KANUN LABARAI
NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

KANUN LABARAI
Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Mukhtar Yahya Usman
Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.
Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.
Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.
Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.
Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.
Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.
Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.
Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.
Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

KANUN LABARAI
Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Aminu Abdullahi
Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.
Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.
Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.
“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.
“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.
Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.
Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.
Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

KANUN LABARAI
A harbe duk wanda aka gani da bindiga kirar AK47-Muhammadu Buhari

Mukhtar Yahya Usman
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin harbe duk wanda aka gani da wasu muggan makamai musamman ma bindiga kirar AK47 mutukar ba jami’in tsaro ba ne.
Kano Focus ta ruwaito cewar jami’in yada labaran shugaban kasar Malam Garba Sehu ne ya bayyana hakan ya yin da ya ke ztawa da sahsin hausa na BBC ranar Laraba.
Garaba Shehu ya ce shugaban kasar ya kuma bada umarnin a ragargaza dukkanin ‘yan ta’addan da suka ki su mika wuya.
Umarnin na shugaban kasa na zuwa ne jima kadan bayan da gwamnoni shida na yankin Arewa suka gudanar da wani taron yadda za su magance matsalar tsaro a jihohinsu.
Haka kuma gwamnonin sun bukaci fito da sabbin dabarun yaki da ga sojojin kasar nan domin dawo da zaman lafiya a yankunann da riki ya di-daita.

-
KANUN LABARAI2 years ago
Budurwa ta kashe kanta a Kano ta hanyar rataya
-
KANUN LABARAI2 years ago
Gwamnatin Kano za ta mayar da ma’aikatan wasu hukumomin ta zuwa makarantu
-
KANUN LABARAI2 years ago
Yadda muka samu silin gashin manzan Allah a Kano-Sheik Karibullah
-
KANUN LABARAI2 years ago
Angwaye a Kano na daga aure saboda hauhawar farashin siminiti
-
KANUN LABARAI2 years ago
Zanga-zanga: yadda aka kashe yarana hudu a Kano.
-
KANUN LABARAI2 years ago
Jin waka na kara imani- Ibrahim Khalil
-
KANUN LABARAI2 years ago
Dalilai biyar da ya sa mata suka fi son namiji mai gemu
-
KANUN LABARAI2 years ago
Zanga-zanga: Ana zargin mutane hudu sun mutu a Kano