Connect with us

KANUN LABARAI

Yanzun nan: Kungiyar ‘yan sahu ta umarci mambobinta su janye yajin aiki

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban kungiyar matuka babura na AKOMORAN Alhaji Mansur Tanimu ya umarci mambobinsu da su janye yajin aikin da suka tsunduma nan take.

Kano Focus ta ruwaito Alhaji Mamsur ya bayar da umarnin jim kadan bayan kammala zaman sulhu tsakanin kungiyoyinsu da hukumar KAROTA da kuma ta NLC ranar Talata.

Ya ce tunda ancimma matsaya tsakanin bagarorin biyu, to sai a fito a koma bakin aiki.

Ya kuma roki mambobin nasu da su yi kokari wajen bin sharuddan da aka gindaya domin kaucewa fadawa wata matsala.

Idan za a iya tunawa dai a yau Talatane kungiyar kwadago ta yi sulhu tsakanin kungiyoyin matuka baburan adai-daita Sahun da kuma hukumar KAROTA.

Yanzu-yanzu: An sulhunta tsakanin jami’an KAROTA da ‘yan Adai-daita Sahu

Ko me yasa ‘yan KAROTA suka kauracewa titinan Kano

KAROTA ta kama inyamuri da ya yi safar tabar wiwi katan 60 zuwa Kano

Yayin zaman na yau an cimma yarjejeniya kamar haka.

‘Yan Adai-daita Sahu za su biya harajin N100 kamar yadda doka ta tanada a kullum amma ba kamar yadda ya ke a bayaba.

Duk wanda zai biya harajinsa to dole ne ya yi Remiter  karon farko domin a dauki bayanan sa a adana.

Haka kuma kowanne dan sahu zai biya na farko a tsakanin makonnin biyu daga ranar 23 ga Fabrairu zuwa 09 ga watan Maris mai kamawa

Haka kuma bayan anyi  biyan farko za a ci gaba da biya na kullum-kullun ta wayar hannu ko kuma ta POS ba kamar a baya ba da sai anje banki.

Duk wanda ya ke so zai iya biyan na kwana daya ko na sati ko kuma na wata-wata ko na shekara amma ba dole bane.

Yana daga cikin abinda aka cimma duk wani dan sahu zai rubuta labar babur dinsa dara-dara a bayan babur dansa.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending