Connect with us

KANUN LABARAI

Yajin aikin ‘yan sahu ya jawowa daliban jami’a maimata shekara

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Yajin aikin matuka baburan Adai-daita Sahu ya jawowa dalibai da dama asarar jarrabawa a jami’o’i da manyan makarantun jihar Kano da hakan ke nuna za su maimaita shekara kacokan.

A zantawar Kano Focus da wasu daga cikin daliban da suka tafka asarar, sun bayyana yadda suka shiga wani hali sakamakon yajin aikin da masu dan Sahun suku shiga.

A cewarsu galibinsu basu samu damar rubuta jarrabawa ba, kuma makarantunsu ba lallaine su duba halin da suka shigaba, balle a ce za a sake yi musu wata daban.

Zahra Jibril Ibrahim da ke sashin ilimin addinin musulunci a jami’ar Yusuf Maitama Sule ta ce duk kokarin da ta yi na taga ta samu yin jarrabawar amma bun ya ci tura.

Acearta ta fito ne tun karfe takwas na safe daga unguwar Ja’en amma har tazo Dorayi karshen waya ba ta samu abin hawa ba.

Ta kara da cewa dakyar ta samu wani mai kurkura  ya dauke ta zuwa makarantar da shima sai da ya karbi N300 a gurin ta.

Ta kuma ce duk da ta hau kurkura amma bata samu damar rubuta jarabawarba saboda kafin ma ta isa makarantar an kammala jarrabawar.

“Muna da yawa wadanda bamu samu damar rubuta jarabawarba amma mun shirya zamuyiwa makaranta korafi ko za ta bamu damar rubutawa,” a cewar ta.

Yajin aikin ‘yan sahu: Kurkura ta maye gurbin adai-daita a Kano

‘Yan adai-daita sahu bata Kano suke -Bappa Babba

Za a kwace adai-daita sahun duk wanda ya fita zanga-zanga

Ita  ma wata daliba Zainab Mika’il dake Jami’ar Bayero, ta ce tun daga Hotoro farawa ta tako da kafa har saida ta zo Hotoro kwanar Magi sannan ta samu wani mai babur da ya rage mata hanya zuwa Kabuga.

Ta kara da cewa daga Kabugane ta samu a kori-kura ta karasa da ita zuwa jami’ar Bayero domin ta rubuta jarabawa.

Ta ce duk da haka lokacin da ta isa makarantar ta tarar an gama jarabawar baki daya.

” Iya daliban da suke zaune a makaranta ne kawai suka samu damar rubuta jarabawar, amma mu da muke zuwa daga nesa ba muyi ba.

“Amma naji shuwagabannin aji sunce za su bibiyi al’amarin danganin an bamu damar rubutawa koda bayan mun gama jarabawa gaba daya ne,” a cewar ta.

Ta ce ya kamata gwamnati tayi abinda ya dace domin wannan yajin aiki ba kowa yake shafaba face ‘ya’yan talakawa da basu da masu kai su makaranta a mota.

Sadiya Aliyu daliba a kwalejin ilimi ta tarayya dake jihar Kano ta ce rashin abin hawa yasa ta rasa rubuta jarabawar da take tsaka dayi.

“Na tarar da yawan dalibai sun fito daga dakin jarabawa kuma da alama na rasa ta kenan, naje don a bani na rubuta amma ance ta riga ta wuceni.

“Ina fata iya wannan ranarce kawai ba za su cigaba da yin yajin aikinba, don kuwa indai aka cigaba da yin haka to tabbas zan ta rasa rubuta jarabawa ta,” a cewar ta.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending