Connect with us

KANUN LABARAI

Masoyana ku janye karar da kuka kai Ganduje-Abduljabbar Kabara

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Malam Abduljabar Nasiru Kabara ya bukaci masoyansa da suka kai gwamnatin Kano kara kan dakatar da shi daga yin wa’azi da rufe masallatansa da su janye karar.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakanne ta cikin wani sakon video da ya wallafa a shafin sa na facebook a ranar Laraba.

Malamin ya musanta cewar ya kai gwamnatin Kano kara bisa dakatar da shi da tayi na cigaba da yin karatu da kuma rufe masallatan sa a jihar Kano.

Inda ya ce masoyansa ne suka shigar da gwamnatin kara bisa kishi da kauna da suke nuna masa.

A don hakan ne man ya  roki masoyan nasa dasu janye karar domin baiwa gwamnati damar kammala binciken da tace ta bada umarni ayi.

Na shirya tsaf domin tunkarar malaman Kano-Abduljabbar Kabara

Yadda rikicin Abduljabbar ya jawowa Ganduje farin jini a Kano

Sarkin Kano ne zai jagoranci mukabalar Abduljabbar a fadarsa- Ganduje

“Idan ba a manta ba na roki gwamnati da ta tabbatar da adalci, kuma matukar akayi adalci zamu karbi abinda akayishi bisa gaskiya don haka babu bukatar zuwa kotu”

“Anyi garaje wajen shigar da karar, kafin jiran wannan hukunci da bincike da akace suna yi,” a cewar sa.

Ya kara da cewa ya zabi ya bayyanawa duniya sakonne domin wasu za suyi tunanin ya yi baki biyu, domin da fari ya ce ba zaije kotu ba kuma a yanzunma masoyan sa ne suka kai kara kotun bashi ba.

Ya kuma ce ya yi iya yinsa don hana su shigar da kara kotu amma saboda damuwa da zullumi yasa suka garzaya kotun.

Ya ce yana fata hukuma za ta yi adalci don tabbatar da dai-daito da zaman lafiya tsakanin al’ummar kasa.

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

KANUN LABARAI

A harbe duk wanda aka gani da bindiga kirar AK47-Muhammadu Buhari

Published

on

Muhammadu Buhari
Share

Mukhtar Yahya Usman

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin harbe duk wanda aka gani da wasu muggan makamai musamman ma bindiga kirar AK47 mutukar ba jami’in tsaro ba ne.

Kano Focus ta ruwaito cewar jami’in yada labaran shugaban kasar Malam Garba Sehu ne ya bayyana hakan ya yin da ya ke ztawa da sahsin hausa na BBC ranar Laraba.

Garaba Shehu ya ce shugaban kasar ya kuma bada umarnin a ragargaza dukkanin ‘yan ta’addan da suka ki su mika wuya.

Umarnin na shugaban kasa na zuwa ne jima kadan bayan da gwamnoni shida na yankin Arewa suka gudanar da wani taron yadda za su magance matsalar tsaro a jihohinsu.

Haka kuma gwamnonin sun bukaci fito da sabbin dabarun yaki da ga sojojin kasar nan domin dawo da zaman lafiya a yankunann da riki ya di-daita.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Ya zama dole a mayar da hankali kan bincikar kasafin kananan hukumomi-Kungiya

Published

on

Share

Aminu Abdulllahi

Wata kungiya mai suna Say No Campaign ta soki yadda al’umma ke mayar da hankalinsu kacokan kan gwamnatin tarayya kan al’amurn  da suka shafi raya kasa.

Kano Focus ta ruwaito shugaban kungiyar Ezenwa Nwagwu ne ya bayyana haka yayin tattaunawa kan yadda al’umma za su bibiyi kasafin kudin kananan hukumomi a ranar Laraba a Kano.

Ya ce kananan hukumomi ma na yin kasafin kudi duk shekara, domim gudanar da ayyukansu, amma al’umma basu damu da bibiyar me suke yi ba.

“Suna maida hankali ne akan gwamnatin tarayya maimakon ayyukan da gwamnatocin su na jiha ko kannan hukumomi ya kamata suyi.

Bama sanya ido akan kananan hukumomi koda ace asusunsu a hade yake dana jihohi amma ana turo musu kudi da za su yiwa al’umma aiki.

“Kuma kudin da yake zuwar musu naku ne ba na aljihun su ba,” a cewar sa.

Ya kara da cewa rashin sanya ido akan kasafin kudin kananan hukumomi da al’umma ke yi yasa shugabannin ke karkatar da kudaden da aka ware don yin ayyuka.

Ya ce dokar ‘yancin samun bayanai ta 2011 ta kasa bata ta’allakaba ga kafafen yada labarai kawai.

Ya ce kowanne dan kasa yana da ikon neman bayani kan wani aiki da ya shafe shi daga gurin gwamnati.

Ya kuma ce matukar al’umma suka hada kansu tare da bibiyar yadda gwamnatoci da ke kusa da su suke kashe kudaden al’umma  shakka babu za a samu raguwar cin hanci da rashawa.

Continue Reading

Trending