Connect with us

KANUN LABARAI

Ina rokon Ganduje ya yi min alfarama-Abduljabbar Kabara

Published

on

Abuljabbar, Gnduje
Share

Mukhtar Yahya Usman

Dakataccen limanin masallacin juma’a na Filin Mushe Abduljabbar Nasiru Kabara ya roki alfaramar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya yi masa adalci.

Kano Focus ta ruwaito Abduljabbar Kabara ya yi rokonne ta cikin sakon murya da ya saki da yammacin ranar Juma’a a nan Kano.

Abduljabbar ya ce yadda yasan Ganduje da kwatanta adalci to yana bukatar ya jajirce ya kuma tsaya akan adalcin nasa.

A bani damar zama da malamai

Abduljabbar ya ce hanyar da za a bi a warware wannan al’amari yana da sauki matukar aka bashi damar zama da malamai aka tattauna.

“Kira da nake ga hukuma musamman ma shi mai girma gwamnan Kano Kadimul Islm, shi ne irin yadda yake kwatanta adalci, to ina rokon da ya dada tsayawa kan turbar adalcin nan.

“Wannan al’amari da ya taso hanyar warwareshi ina ganin mai sauki ne, idan aka yi amfani da tsarin zama, kamar yadda Allah ya fada ‘kul-haatu-burhanukum’.

Bana zagin sahabbai

Abduljabbar ya ci gaba da ce zargin da ake yi masa na zagin sahabbai ko kandan ba gaskiya ba ne

“Wadannan bayin Allah suna cewa ana fadar maganganu na cin zarafi ko ga janibin ma’aiki, ko ga janibin Sahabbai, wanda ni kuma ina ganin ko kusa ba haka bane.

“Wadannan maganganu ni musasu ma nake, a cikin littattaifai suka zo, kuma littattafan akwaisu a ko ina, bankaraba ban rageba ban canzaba.

“Mai girma gwamna ya yi adalci , malamanan in da gaske suke cewa ina batanci ga ma’aiki, wadannan maganganu ni nake fadarsu ba a littattafai suke ba su yadda mu zauna.

“Duniya ta saurara  zan taho da littattafannan na fito da maganganun nan su kuma su taho da nasu su nuna babu, ko abinda banganeba su ganar da ni.

Ina so a nunamin kuskurena

Dakataccen limin ya ci gaba da cewa yana matukar murna idan aka fahintar da shi kuskure ya ke yi kuma zai karaba ya gyara inda ya tabbata.

“Kullum ina fadan tunkafin ma abu yayi zafi haka, nifa murna nake yi ma a sami wanda zai zo ya nunamin abinda ya fi nawa.

“Kuma fahintar nan a baya akanta nake kuma ba da dadin rai na bartaba ba.

Ina murnanar na fahinci cewa abinanda neke kai a baya shi ne gaskiya.

“Da zuciya daya Allah shi ne shaida, idan suka yi wannan kokarin muka zauna suka fahimtar dani wani abu da ban fahinta ba, suna da alkawari a guna na karbar abinnan kai tsaye.

“Ga kuma babban lada da suke dashi na shiryar da dauwansu musulmi.

Gwaman ka yi adalci

Ya kuma bukaci gwaman Kano Abdullahi Ganduje da ya yi adalci kan batun tsakaninsa da sauran malamai.

“Don haka kirana ga mai girma gwamnan Kano ya yi kokarin tsayar da adalci tsakanina da masu tuhume-tuhume.

A shirya zama na mutunci cikin lumana cikin mutunta juna maganganunnan a tattauna.

“Wanda ya ke da kaikayi kan wata magana da yake ganin ba haka take ba yazo da littafinsa da take ciki ni kuma zanzo da littafin da take ciki mu tattauna sannan ayi alkalanci.

Mabiya su bi abida hukuma ta ce

Abduljabbar Kabara ya kuma nemi alfarmar al’umma musamman ma magoya bayan sa da su zauna lafiya banda tashin hakali.

Ya ce su yi kokarin yin biyayya ga dokar da gwamnati ta kafa na hanashi karatu.

Ya kuma bukacesu da su kaucewa tashi hankali da husuma har a kammala binciken da akace a na yi.

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending