Connect with us

KANUN LABARAI

‘Yan Film basu tallafawa Ashiru Nagoma ba-Abokanansa

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Shekaru 10 kenan da fitaccen daraktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya kamu da cutar tabin hankali, amma abokan aikinsa na film ko kadan basu wai-wayeshi ba.

A wata zantawa ta musamman da jaridar Kano Focus ta yi da ‘yan uwa da abokan Nagoman, sunce ko kadan babu wani daga cikin ‘yan film da ya yi yunkurin tallafa masa tun bayan da ya kamu da cutar.

Kabiru Abubakar Yusuf Abokine na kud-da-kud ga daraktan ya ce Nagoma ya kwashe shekaru da dama yana fama da cutar.

Yace tun mahaifan daraktan na raye suke ta dawainiya da shi wajen ganin al’amuransa sun dai-daita.

Sai dai dukkaninsu sunbar duniya da burin ganin Nagoman ya samu lafiya kamar kowa.

Kabiru ya ce tun bayan mutuwar iyayensane kuma ‘yan’uwa da abokan arzki suka rungumi lamarinsa.

“Muna ta kokari wajen ganin mun samo kansa amma dai babu wani dan filim da ya zo koda wasa ya ce yana son taimaka mana.

Shima wani Aboki ga daraktan  Habibu Ibrahim Umar ya ce sun sha fama da abokin nasu kuma suna kan sha har yazu.

Ya ce amma batun wasu daga cikin yan film sun tallafa masa abune da ba zai iya tunawa da shi ba, duk da cewa ba abinda ya ke boyuwa a gareshi na marar lafiyar.

Yace hana karya guda daga cikin yam fima Adam A Zango ya taba cewar zai tallafa masa, shima bayan da suka nuna bukatar ya taimaka.

“Tun muna yara muke tare da Nagoma, har kawo yanzu muna tare da shi.

“Muna tare ya shiga film, kuma muna tare dukkanin matsalar ta sameshi, kuma har yanzu muna tare tunda namune.

“Naji ana ta cewa yan film sun tallafa masa, ni dai a iya sani na ba wani dan film da ya tallafa masa, hasalima tunda ya samu matsalar suka watse.

Shima Umar Muhammad da baccine ke rabasu da daraktan ya ce ya kalubalanci duk wani dan film da ya ce ya tallafawa Nagoman.

A cewarsa sun sha tura neman tallafinsu ga abokana sana’artasa, amma suna bada musu kasa a ido.

Kokarin jin tabakin masu madafan iko a kungiyar yan fim ta jihar Kano MOPPAN ya ci tura, biyo bayan dukkanin wayoyin su da aka buga basu dauka ba.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending