Connect with us

KANUN LABARAI

KAROTA ta kama inyamuri da ya yi safar tabar wiwi katan 60 zuwa Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar KAROTA ta kama wani inyamuri Mista Ekennah Okechuku da ya yi safarar kwalaye sama da guda 60 dake dauke da tabar wiwi zuwa jihar Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewa hukumar ta kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan da ya boye tabar a cikin motar safa.

Wanda ake zargin ya fito ne daga jihar Imo  ya ce yana safarar magungunan daga Lagos zuwa Kano inda yake kai wa kwastomominsa.

Haka zalika mista Okechuku sunansa na cikin jerin sunayen da hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) take nema, bisa aikata laifin dillacin tabar wiwi zuwa Kano.

A yayin mika wanda ake zargin ga Kwamandan, NDLEA, shugaban hukumar Karota Baffa Babba Dan’agundi yace hukumar sa ta ba da umarnin sauya gurin zama na tashar motar Sabon Gari da ake kira  (Luxurious Buses) saboda irin wadannan laifuka da ake aikatawa da irin wadannan motoci.

KAROTA ta baiwa ‘yan kasuwar katako awanni 44 da su bar bakin titi

Hukumar KAROTA za ta tara harajin sama da miliyan dubu a shekar 2021

Akwai lada ga wanda ya kawo tsurkun miyagun ayyuka a Kano -KAROTA

Ya kara da cewa umarnin ya fara haifar da da mai ido dan kuwa wasu kamfanonin motocin na hada kai da KAROTA don tona asirin duk wani mutum ko gungun mutane da ke safarar haramtattun kayayyaki zuwa Kano.

Ya kuma yi gargadin cewa duk kamfanin da aka samu da laifin hada baki da wasu marasa kishi wajen aikata laifi a jihar nan  to za a kwace motar su tare da korar kamfanin daga jihar baki daya.

A nasa bangaren Kwamandan, NDLEA, a nan Kano Ibrahim Abdul ya yi godiya ga KAROTA bisa hadin kan da ke tsakanin hukumomin biyu wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin.

Ya ce a baya rundunar ta cafke wasu kayayyaki guda biyu na mutumin wanda ya yi amfani da dabaru wajen boye su a cikin wasu buhunna wanda hakan yasa aka gaza kamashi.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending