Connect with us

KANUN LABARAI

Yadda muke komawa alarammomi domin mu damfari jama’a a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Kungiyar tsaro ta Vigilante da ke Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni ta kama wasu ‘yan damfara uku da suke fakewa da addini suna damfarar mutane.

Kano Focus ta rawaito jami’an Vigilante din sun kama su ne ranar Litinin a tashar Unguwa Uku lokacin da suke tsaka da aikata damfarar tasu.

Wadanda aka kama din sun hadar da Aminu Abubakar da Abdullahi Sulaiman da Nura Adamu.

Da yake amsa tambayoyin jami’an tsaron Aminu Abubakar wanda  dan asalin garin Doran Baga ne da ke jihar Borno ya ce ya zo Kano ci rani ne kuma ya buge da damafara.

Ya ce ya samu wasu da suka kware akan damfarar ne a tashar Unguwa Uku sai kawai ya hada kai da su, suka koya masa yadda ake yi.

“Muna fakewa ne da cewa mu malamai ne yadda, muka samu yan koro da ke dafe mana baya, sai  muje mu samu mutum mu nuna masa mu din yan baiwa ne. Sann mu yi masa wani abun al’ajabi da zai ja hankalisa har ya saurare mu.

“A kalla na damfari mutum bakwai, na karbi waya kirar blackberry da naira dubu tara haka kuma na sake karbar waya kirar Tecno Comon a hannun wani na kuma karbi ViVo da dai sauran su,” a cewar sa.

Damfarar mata akwai wahala

Sai dai Aminu ya ce suna matukar tsoron mata wajen yin damfarar ta su domin kuwa mata basu da dadin sha’ani.

A cewarsa hakan ce ma ta sanya mafiya wadanda suke tunkara da sana’ar ta su maza ne.

Shima daya dan damfarar Abdullahi Sulaiman Unguwa Uku ya ce bai fiye damfara a jihar Kano ba.

Ya kara da cewa a kallah ya damfari mutane talatin da suka hada da kudi da wayoyin hannu.

Ya kuma ce suna da yawa masu aikata sana’ar damfara a Kano, sun kuma bazu a unguwanni daban-aban.

Nura Adamu Gyadi-Gyadi dake sana’a a kasuwar Farm Center kuma daya daga cikin yan damfarar da ke siyan wayoyin da aka damfaro ya ce yana siyan waya a gurin su duk da yasan ta damfara ce.

Sai dai ya ce tsautsayi ne ya sa shi yake siyan wayoyin satar a hannun su.

Da yake nasa jawabin shugaban Vigilante na unguwar ‘Yan Awaki Adamu Abubakar ya ce wadanda ake zargin sun dade suna addabar titin uguwar ‘yan awaki.

Ya ce suna tare mata tare da karbe musu kudade da wayoyi da sunan za su yi musu rokon Allah.

Ya kara da cewa a makon da ya gabata suka damfari wani yaron shago kudi naira dubu dari tara tare da karbe wayar sa.

Ya kumace sun fara kama mutum daya ne a cikin su wanda ta hanyar sane suka kama ragowar wadanda ake zargi.

Ya kara da cewa tuni suka mika wadanda ake zargin ga hukumar ‘yan sanda domin girbar abinda suka shuka.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending