Connect with us

KANUN LABARAI

Mun biya kudaden tallafin karatun da gwamnatin Kwankwaso ta kasa biya-Ganduje

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Gwamnatin Kano ta ce ta kashe naira biliyan daya da miliyan dari takwas wajen biyan kudaden tallafin karatun daliban jihar Kano da ke karatu a jami’o’I masu zaman kansu a fadin kasar nan da gwamnatin bayan ta kasa biya.

Kano Focus ta ruwaito gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne yayin mika shahada ga dalibai 20 ya yin zaman majalisar zartaswa ta Kano a ranar Laraba.

Daliban da aka mikawa shaidar sun kammala karatunsu ne a jami’ar AUN Yola, inda biyu suka samu shaidar kammala karatu ta farko wato (first class) ya yin da 18 kuma suka samu mataki na biyu.

A cewar Ganduje daliban suna cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta dauki nauyin karatun su, amma ta biya musu kaso goma ne kawai na abin da ya kamata a biya.

a cewarsa sai dai gwamnatinsa ta zo ne kuma ta bibiyi al’amarin ta kuma ci gaba da biyan kudin daliban.

Jamio’in da gwamnatin ta tura daliban sun hadar da American University of Nigeria (AUN) Yola, sai kuma Jami’ar Crescent da jami’ar Alkalam da ke Katsina, da kuma jami’ar Bells  da ta Igbinidiom Okada.

Da yake taya daliban da suka kammala murna gwamnan ya bukaci su yi amfani da abinda suka koya yanda ya da ce ta yadda al’umma za su amfana da su.

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending