Connect with us

KANUN LABARAI

Dalibai su koma hadiman masallatai da coco-coci maimakon jiran gawon shanu-ASUU

Published

on

Share

Zulaiha Danjuma

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta bukaci dalibai da su koma hadiman masallatai da coci coci maimakon zaman jiran gawon shanun yaushe za a bude makarantu.

Haka kuma ta bukacesu da su rungumi sana’o’in dogaro da kai da karance-karancen littattafai da kuma yawon bude idanu maimakon zaman jira bude makarantu.

Kano Focus ta ruwaito cewar kungiyar ta wallafa wananan kiranne a shafinta na twitter a ranar Alhamis.

ASUU ta zayyano abubuwa bakwai da ya kamata daliban su runguma maimakon zaman jiran gawon shanu.

Ta ce ya kamata daliban su nemi aikin yi nawucin gadi da za su dinga samun dari da kwabo,

Haka kuma tace wadanda ‘yan uwansu ke da wata sana’a to su shiga a dama da su domin rage zaman banza.

ASUU ta ce akwai bukatar daliban su koyi wasu dabarun sana’o’I na zamani da zai ciyar da su gaba.

Haka kuma ta ce wanda basu da iko su lazamci zuwa masallaci ko kuma coci domin taimakawa addini.

Ta ce wasu daliban kuma da suke da dama su rungumi yin tafiye-tafiye domin kwakwalensu su bude.

Yayin da wasu kuma ya kamata su rungumi karatun littafi, sai shawara ta karshe shi ne wadanda ke da dama kuma su shiga rakashewa da jin dadin duniya ta hanyar kallon fina-finai da zuwa sinima domin kansu ya bude

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending