Connect with us

LABARAI

Rundunar ‘yan sanda ta musanta kashe matashi a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta musanta zargin da ake mata na kisan wani matashi mai suna Saifullahi Sani a unguwar Kofar Mata dake birnin Kano.

Kano Focus ta ruwaito cewar wannan na kunshe ne cikim wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar litinin.

Sanarwar ta ruwaito kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu A Sani na cewa hukumar ta samu sanarwa cewa ‘yan daba na fada a unguwar Kofar Mata a jiya Lahadi.

A cewar sa hakan ce ta sanya runudunar ta tura jami’anta domin dai-daita al’amura.

Yace yayin kai daukin ne hukumar ta samu nasarar kama mutum biyu da ake zargi, rike da wukake.

Ya ce Hukumar ta kama matshi ne bayan da tuni aka soke shi da wuka a jikinsa tare da wani jami’in dan sanda.

Bayan da aka kai shi asibiti ne kuma ya mutu a can, inda shi kuma dan sandan aka mai da shi wani asibitin domin ci gaba da karbar magani.

Idan ba a manta ba a yau litinin ne al’ummar yankin Kofar Mata suka  fito zanga -zanga dan nuna fushin su kan zargin da suke yiwa jami’an ‘yan sanda na kashe wani matashi  Saifullahi Sani Musa mai shekaru 23.

matasa da dama ne suka mamaye titin Kofar mata da kewaye suna kona tayoyi tare da hana jama’a wucewa domin nuna adawar su da kisan matashin.

mahaifin matashin Sani Musa Kofar Mata ya shaidawa Kano Focus cewa da misalin karfe daya na dare jami’an yan sanda suka kai sumame unguwar suka kuma kama dan nasa lokacin da yake bacci a kofar gida.

Mista Musa ya kara da cewa bayan da gari ya waye yana kokarin tafiya ofishin yan sandan ne guda daga cikin yan kwamitin unguwar ya shaida masa cewar yan sanda sun kashe dan nasa.

Ya kara da cewa dan kwamitin ne ya shaida masa gawar dan nasa tana sashen bada agajin gaggawa na asibitin murtala amma za su kaita dakin ajiyar gawawwaki.

Malam Musa yace akwai raunukan duka da dama a jikin yaron da yake zargin jami’an ‘yan sanda sunyi masa.

Shima wanda ke tare da mamacin a lokacin da jami’an ‘yan sandan suka zo samamen Hamisu Muhammad yace suna bacci yayin da ‘yan sandan suka zo.

ya kara da cewa daga nan ne suka yi yinkurin tafiya dasu wanda shi kuma yasamu nasarar tsarewa.

To sai dai rundunar yan sadan ta musanta wannan zargi inda ta ce kokadan bata da hannu kan kisan matashin.

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

KANUN LABARAI

Darakta Ashiru Nagoma ya samu lafiya

Published

on

Share

Mukhtar Yahya Usman

Fitaccen darktan shirya fina-finan Hausa Ashiru Nagoma ya fito daga Asibiti bayan da likitoci suka tabbatar da samun lafiyarsa.

Kano Focus ta ruwaito an sallamo shi daga asibitin ne da yammacin yau Alhamis.

Idan za a iya tunawa dai tun a ranar 14 ga watan Janairu ne ‘yan uwansa da kuma kungiyar Fauziyya D Sulaiman suka kai shi asibiti, bayan anyi zarigin yana da tabun hankali.

Rahotannin sunyi nuni dacewa Nagoma ya shafe kimanin shekaru goma yana dauke da cutar tabin hankali.

Ko da yake al’umma da dama na ganin ba cutar tabin hankali ke damunsaba illa ta damuwa, ciki kuwa har da ‘yan uwansa.

Haka zalika makwanni shida ke nan kungiyar jin kai ta Fauziyya D Sulaiman da hadin gwiwar ‘yan uwansa suka garzaya dashi asibiti domin duba lafiyarsa.

Acewar dan uwa ga darktan Kabiru Abubakar Yusuf, Ashiru Nagoma ya samu lafiya sumul har ma an sallamoshi daga asibiti.

Kabiru Abubakar ya kuma mika godiyarsa ga dukkanin wadanda suka tallafa wajen samun lafiyar tasa, musamman Fauziyya D Sulaiman da kuma rukunnan Abokanansa Baki daya.

Haka zalika ya ce suna godewa duk wanda ya tallafa musu da addua wajen ganin dan uwan na su ya samu lafiya.

Continue Reading

KANUN LABARAI

NAFDAC ta kone jabun kayayyaki na milyan 600 a Kano

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Hukumar lura da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) to kone gurbatattun kayayyaki na sama da naira miliyan 600.

Kano Focus ta ruwaito cewa an gudanar da kone kayayyakin ne ranar Alhamis  a garin Hawan Kalewawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano .

Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, daraktan hukumar shiyyar arewa maso yamma Dauda Gimba ya ce kayayyakin da aka kone sun hada da wandanda basu da rijista da kuma jabun kayayyaki da aka kamasu a jihar Kano da Kaduna.

Haka kuma wasunsu an an kama ne a jihohin Jigawa Katsina.

Sokoto da Zamfara sai jihar Kebbi.

Ya ce anyi hakanne don a tabbatar da cewa kayayyakin basu koma kasuwa ba don kar wasu su sake siyan su.

Ya kuma ce sun zabis u kone kayayyakin ne a jihar Kano sakamakon a nanne aka fi samun gurbatattun kayayyakin da ake siyarwa al’umma.

Ya ce al’umma su tabbatar da cewa duk abinda za su siya yana dauke da shaidair hukumar NAFDAC don gujewa yin amfani da abinda zai cutar da lafiyar su.

Continue Reading

KANUN LABARAI

Tuhumar Abduljabbar za a yi ba mukabala ba-Sheikh Ibrahim Khali

Published

on

Share

Aminu Abdullahi

Shugaban majalisar malamai ta jihar Kano Malam Ibrahim Khalil ya ce za a tuhumi Abduljabbar Kabara ne kan abubuwan da yake furtawa amma ba mukabala za a yi da shi ba.

Kano Focus ta ruwaito cewa malamin ya bayyana hakane a ranar Alhamis ya yin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce za a zauna da shi ne a tuhume shi kan irin fatawoyin da yake bayarwa sabanin yadda mutane ke zaton cewa mukabala za ayi.

“Idan aka kira shi mukabala an canja masa ma’ana mutane suna cewa mukabala-mukabala, ba mukabala ba ce tuhuma ce.

“Tuhumar ita ce, ka ce abu kaza da kaza, to waye ya yi wannan bayanin a malamai, kamar yadda ka yi shi, a malamai na Musulunci waye kuma ya yi wannan fasarar da ka yi shi.

Ita kuwa mukabala ita ce kai kana cewa kaza wancan yana cewa kaza to sai a zo a zauna tsakanin naka da nasa wanne ne ya fi, shi ne za a yi mukabala, don a ga wanda nasa ne ya fi zama dai-dai,” a cewar sa.

Ya kara da cewa an dade ana kawo rigingimu daban-daban na fahimtar addini a jihar Kano amma ba a taba ganin irin fahimtar da Abduljabbar ya zo da ita ba.

Ya ce shi kansa mahaifinsa Malam Nasiru Kabara, bai taba hawa irin wannan turbar da ‘dan nasa ya hau ba.

Continue Reading

Trending